HomeMusic Video
cheatstutorials news

Kungiyar Real Madrid tana duba yiwuwar sayar da Cristiano Ronaldo ga kulob din Juventus a kan kudi fam miliyan 88.
Dan wasan na Portugal mai shekara 33, ya ci wa Madrid kwallaye 451.
Madrid ta kammala gasar La Ligar bara ne a matsayi na uku, inda abokiyar hamayyarta Barcelona ta lashe gasar.
Ronaldo ya lashe Kofin Zakarun Turai karo na biyar tare da kungiyar Madrid a watan Mayun da ya gabata.
Bayan wannan nasarar ne kocin kungiyar Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa kuma aka maye gurbinsa da tsohon kocin kasar Spain Julen Lopetegui.
Dan wasa ronaldo dai yazo kungiyar real madrid ne daga manchaster united akan kudi fam miliyan 80 a 2009..
Wata majiyar tana ganin cewar realmadrid tana shirin maye gurbin ronaldo da danwasan gaba na kungiyar psg wato kyllian mbappe

Post a Comment

 
Top