HomeMusic Video
cheatstutorials news

Wata babbar kotu a Najeriya ta amince da bukatar da wasu lauyoyi suka shigar na bai wa majalisar dokokin kasar umarnin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Alkalin babbar kotun da ke garin Osogbo jihar Osun, Mai shari'a Onyetenu ce ta bayar da umarnin a ranar Laraba, bayan da wani lauya - Kanmi Ajibola da Sulaiman Adeniyi wani dan rajin kare hakkin dan Adam suka bukaci kotun ta dauki wannan matakin.
Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na Buhari na daga cikin bukatu hudu da mutanen biyu suka gabatar a gaban kotun, inda suke zargin shugaban da saba wa kundin tsarin mulkin kasar bayan rantsar da shi da takardun da suka kira na bogi.
Sai dai tun lokacin yakin zabensa ne kwalejin gwamnati a Katsina, inda Buhari ya kammala sakandare ta fitar da takardar shaidar kammala karatun a shekarar 1961.
Zuwa yanzu gwamnatin Buhari ba ta ce komi ba game da batun, sannan majalisar dokokin kasar ma ba ta ce komi ba zuwa yanzu.
Lauyan da ya shigar da karar Mista Kanmi Ajibola ya shaidawa manema labarai cewa kotun ta amince da bukatar ne bayan gamsuwa da hujjojinsa.
Ya ce: "Kotu ta ba ni hurumi a kan karar da na shigar inda na nemi a tilasta wa majalisun dokoki biyu na Tarayyar Najeriya da su fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari."
Mutanen biyu sun ruga kotu ne bayan majalisa ta yi biris da bukatar farko ta tsige Buhari da suka shigar watanni uku da suka gabata.
Sauran bayanan da suka gabatar a gaban kotun da suke kalubalantar Buhari sun hada da gazawar gwamnati wajen kawo karshen yawaitar kashe-kashe a rikicin makiyaya da manoma.
Sannan sun zargi shugaban da yin gaban kasa wajen kashe kudin kasa ba tare da amincewar majalisa ba.
A cikin bayanan da suka gabatar wa kotun, sun ce "shugaban ya yi rantsuwa cewa zai mutunta kundin tsarin mulki da kare rayuka da dokiyoyin 'yan kasa."
"Na kafa hujja a gaban kotu kuma bayan gamsuwa da karar cewa shugaba Buhari ya gaza wajen kawo karshen kashe-kashe a kasar, kotu ta ba da umarnin a tsige shi" in ji Akanmi.
Kotun ta dage sauraron wannan karar zuwa 30 gawatan oktoba 2018..

Post a Comment

 
Top