HomeMusic Video
cheatstutorials news

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya lashi
takobin cewa zai dukufa wajen ganin an ceto
yarinya daya tilo da ta rage daga cikin yammatan
makarantar Dapchi 110 da aka sace, kamar yadda
ya yi a lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya lashi
takobin cewa zai dukufa wajen ganin an ceto
yarinya daya tilo da ta rage daga cikin yammatan
makarantar Dapchi 110 da aka sace, kamar yadda
ya yi a lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram.
A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na
musamman a kan harkokin watsa labarai Malam
Garba Shehu ya fitar, ta ce, gwamnatin shugaba
Buhari, ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ganin
ta ceto tare da dawo da yarinyar mai sauna Leo sharibu, gida wajen
iyayenta lami lafiya, kamar yadda aka ceto sauran
yammatan, bayan da 'yan ta'addar suka rike ta
kamar yadda aka rawaito cewa saboda ta ki yar da
ta musulunta ne.
Sanarwar ta ce, shugaba Buhari, na cike da sanin
nauyin da ya rataya a wuyansa, kamar yadda tsarin
mulkin kasar ya tanadi ya kare dukkannin 'yan
Najeriya, ba tare da la'akari da bambancin
addininsu ko kabilarsu ko kuma yankin da suka fito
ba, kuma ba zai gajiya ba wajen sauke wannan
nauyi.
Kazalika sanarwar ta ce, shugaban na sane da
fadar cewa, dukkannin musulmai na gaskiya a fadin
duniya, suna martaba ka'idar nan da ke cewa babu
tilas a addini.
A dangane da haka, babu wani mutum ko wata
kungiya da za ta tilasta addininta a kan wani.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugaban na
Najeriya, na cike da alhini ga iyayen wannan
yarinya, wadanda za su rinka kallon sauran
takwarorinsu da aka sako 'ya'yansu na murna,
yayin da su kuma 'yarsu har yanzu ba ta tare da su.
Daga karshe sanarwar ta ce, shugaba Buhari, ya
jaddada cewa ba za a yi watsi da wannan yarinya
da ta rage ba, kuma nan bada jimawa ba, iyayenta
za su kasance cikin murna tare da 'yarsu.
A watan jiya ne dai aka sace yammatan, lamarin da
ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an
tsaron Najeriya.
A ranar Jumma'a ne ake kyautata zaton shugaba
Buharin, zai karbi yammatan na Dapchi a fadarsa
da ke Abuja.

Source: BBCHAUSA

Next
Newer Post
Previous
This is the last post.

Post a Comment

 
Top